You are here

Yadda Ake Salla

×

Error message

Deprecated function: Function create_function() is deprecated in views_php_handler_field->pre_render() (line 202 of /var/www/drupal7-websites/sites/all/modules/contrib/views_php/plugins/views/views_php_handler_field.inc).

 1. Niyya: 

Niyya sharaxi ce, na aingancin salla. Abin da ake nufi da ita kuma shi ne, mutum ya qudurce a cikin birnin zuciyarsa, cewa zai bauta ma Allah ne, da wannan salla ta Magariba ko Isha’i, maslan. Amma, buxa baki ya furta wannan niyya, ba Shari’a ne ba. Iyakar abin da Shari’a take nema daga gare shi, shi ne, zuciya da tunani da qwaqwalwarsa su zama, suna sane da haka. Amma, furta cewa na yi niyyar yin salla kazá, ba a samo hakan daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam,  ko wani dga cikin sahabbansa masu girma, ba. 

 1. Tsayuwa: Bayan niyya kuma, sai ya tashi tsaye don gudanar da salla, ya ce: ‘allahu akbar’  a daidai lokacin da yake xaga hannuwansa sama zuwa ga kunnuwa da kafaxunsa tare das a tafin hannuwan su fuskanci alqibla.   

Ba ya kuma halsata a yi amfani da wani lafazi a matsayin kabbara, wanda da wannan da aka ambata a sama ba, wato: ‘allahu akbar.’  Ma’anarsa kuma ita ce, nuna girma da xaukar da Allah Maxaukakin Sarki yake da su; duk wani abu, wanda da shi ba subhanahu wa ta’alah, to, ya fi shi girma da xaukaka. Duniya gaba xaya da abin duk da yake cikinta na jin daxi, idan aka kwatanta su da Allah Mahalicci, to, ba komai ba ne su. Saboda haka, sai mu ajiye gaba xayan wannan jin daxi a gefe xaya, mu fuskanci Allah Maxaukakin Sarki a cikin wannan salla, muna masu qasqantar da kai, da zuciya da hankulanmu. 

 1. Sa’annan bayan wannan kabbara, sai ya xora hannunsa na dama a kan na hagu, tare da cigaba da yin haka a duk lokacin da ya sami kansa a tsaye cikin halin salla. 
 1. Abin da zai biyo baya kuma, bisa mustahabbanci, shi ne addu’ar buxewa, wato: “subhanakal-lahumma wa bi hamdika, wa tabarakas-muka wa ta’alah jadduka, wa la ilaha gairuka.” 
 1. Sai kuma ya qara da cewa: “a’uzu billahi minash shaixanir rajim”. Waxannan kalmomi kuma su ake cewa isti’aza, wato, neman tsari. Ma’anarsu kuma ita ce: ‘ina fakewa wurin Allah tare da neman tsari daga sharrin Shaixan.’   
 1. Sa’annan kuma ya ce: ’bismillhir-rahmanir-rahim.” Wannan kuma ita ake ce wa ‘basmala.’ Ma’anarta kuma ita ce: ‘ina farawa  da neman agaji da albarka, da sunan Allah.’
 1. Sa’anna ya karanta surar Fatiha, wato, alhamdu. Ita Fatihar nan kuma, ita ce sura mafi girma da xaukaka a cikin littafin Allah. 
 • Saboda girma da xaukakar wannan suta ta fatiha ne, Allah Maxaukakin Sarki ya kwankwanta wa Manzon ni’imar da take cikin saukar masa da ita, da cewa: “Kuma lalle haqiqa, mun ba ka bakwai waxanda ake maimaitawa, da Alqur’ani mai girma”[Hijir:87]. Bakwai xin na kuwa da ake maimaitawa su ne wannan sura ta Fatiha. An kuma ba ta wannan suna ne, saboda ayoyin cikinta guda bakwai ne. Ga shi kuma Musulmi na maimaita karatunta da yawa a cikin kowace rana.  
 • Wajibi ne a kan kowane Musulmi ya koyi yadda ake karanta wannan sura, saboda irin yadda ya zama wajibi ga duk wanda yake salla, ya karanta ta, daxa shi kaxai yake yi, ko tare da liman. Illah dai ba zai karanta tab a a cikin sallar da limaminsa yake karatu bayyane. 
 1. An kuma shar’anta masa cewa ‘ámin’ bayan qare karatun Fatiha xin nan, ko saurarrenta daga bakin limaminsa. Ma’anar ‘amin’ xin nan kuma shi ne: ‘Allah ya karvi abin da liman ya roqa.”
 1. Bayan karatun Fatiha kuma, sai ya karanta wasu surori na daban, amma bayan raka’o’i biyu na farko kawai. Ita kuwa raka’a ta uku da ta huxu, ba zai qara komai a kan Fatiha xin ba.
 • Fatiha da Surar da zai karanta, zai karanta su ne a bayyane, a cikin sallar Subahin da Magariba da kuma Isha’i. Amma, sallar Azahar da ta La’asar, ana karatu a cikinsu ne asirce.
 • Haka kuma sauran gaba xayan rukunna salla, ana karanta duk abin da za a karanta a cikinsu ne a asirce.

 1. za ta xauke shi zuwa ga ruku’i, bayan ya xaukaka hannuwansa zuwa dabra da kunnuwa ko kafaxunsa, inda zai saka cikin tafinsu yana kallon alqibla, kamar dai yadda ya yi a yayin kabbara can ta farkon farawa.
 1. Sa’anna ya shiga ruku’i.

Shi kuwa ana yinsa ne ta hanyar karya qashin baya tare da sunkuyawa gabas, inda gadon bayan nasa da kansa za su daidaita. Hannuwansa kuma zai xora su ne a kan guwawunsa, sa’annan ya ce: ‘subhana rabbiyal’azim.’ Wannan tasbihi da zai kuma, an so ya maimaita shi sau uku, saboda ruku’i, wuri ne wanda a cikinsa ake gimamawa tare da cimcimta Allah Maxaukakin Sarki.

Wannan kalima ta ‘subhana rabbiyal’azim’ kuma, ma’anarta ita ce: ‘Na yi imani tare da tabbatar  da cewa, Allah Maxaukakin Sarki mai tsarki, da girma, da xaukaka ne; babu wata tawaya tare da shi. Ga ni kuma gabanka ya Ubangiji!  Kaina qasa ina ruku’i da taulahi zuwa gare ka, Maxaukakin Sarki.’ Wannan shi ne…

 1. Sa’anna ya xaukako daga wannan ruku’i, 

ya yi tsaye, yana xage da  hannuwansa zuwa dabra da kafaxunsa, cikinsu yana fuskantar alqibla, kamar yadda ya yi a can baya. Sa’anan ya ce: ‘sami’allahu liman hamidah.’  Kar a manta! Za a faxi haka ne, daxa mutum yana sallar shi kaxai ne, ko tare da liman. Sa’anna sai kuma ya ce: ‘rabbana wa lakal-hamdu.’ An kuma so bayan haka ya qara da cewa: ‘hamdan kasíran xayyiban mubárakan fíhi, mil’assamá’i wa mil’al’ardhi wa mil’a ma shi’ita min shai’in ba’ad.’’ 

 1. Bayan haka sai ya surmuyo qasa, tare da kabbara ya faxi ya yi sujada da gavovinsa guda bakwai, 

waxanda suka haxa da goshi, da hanci, da hannuwa, da guwawu, da qafafu. An kuma so ya yi iyakar qoqari kada hannuwan nan nasa su tavi kuivinsa. Cikinsa kuma kada ya tafi cinyoyinsa. Haka zai yi a cikin kowace sujada.Sauran abin da yake tsakanin wuya da guiwar hannunsa kuma, an so kada ya bari su tavi qasa. 

 1. A cikin sujadar nan kuma, 

sai ya riqa faxar: “subhana rabbiyal-a’alah.”  Ita ma wannan kalima, an so ya maimaita ta sau uku. 

Ma’anar waxannan kalmomi na “subhana rabbiyal-a’alah” kuma ita ce: ‘Na yi imani tare da tabbatar  da cewa, Allah Maxaukakin Sarki mai tsarki, da girma, da xaukaka ne, sama da duk wani nau’i na nakasa da aibi. Haka kuma waxannan kalmomi qunshe suke da ayarin tunatarwa, ga mai sujada xin nan, a daidai lokacin da yake can rungume da qasa, yana baza qasqanci da bajewa gaban Ubangijinsa. Eh! tabbas tunatarwa ce gare shi a kan banbacin da yake akwai tsakaninsa da Ubangiji mahaliccinsa. Saboda haka lalle, wannan hali da yake ciki na qanqan da kai zuwa ga Ubangiji kuma majivincin al’amarinsa, daidai ne.
Wannan lokaci kuma na sujada, yana xaya daga cikin manya-manyan lokutan da Allah Maxaukakin Sarki yake karvar addu’a a cikinsu. Saboda haka, bayan wancan zikiri na wajibi da aka ambata, yana da matuqar kyau, muslmi ya roqi Allah dukan alhairin da yak enema na duniya da Lahira. Tabbacin wannan kuwa shi ne faxar Annabi sallallahu alaihi wa sallam: “Babu lokacin da bawa yake kusa-kusa da Ubangijinsa kamar lokacin da yake sujada. Saboda haka ku yawaita roqon Allah a ciki.”[Muslim:482]

 1. Bayan haka kuma sai ya ce:

Allahu Akbar,’  ya kuma zauna tsakanin sujadar farko da ta biyu. Idan kuma zai zaunawa xin nan, an so ya zauna a kan qafarsa ta hagu tare da kafe ta dama, qasa. Sa’annan ya xora hannuwansa a kan goshin cinansa, idan ya baro guwawu. 

 • Duk wani zama da za a yi a cikin salla, haka aka fi son a yi shi, amma. Ban da zaman tahiya ta biyu; yana iya kafe qafarsa ta dama kamar koyaushe, amma ta hagu, sai ya fitar da ita can qarqashinsa, a qasa. 
 1. A lokacin da yake zaune tsakanin sujada biyu xin can, sai ya ce: ‘rabbig-fir lí.’ An kuma so ya maimaita hakan sau uku.
 1. Sa’anna ya zarce ya yi wata sujada kamar yadda ya yi ta farko.
 1. Sa’annan ya taso daga wannan sujada, ya miqe tsaye yana faxar: ‘Allahu Akbar.’
 1. Yadda ya yi wannan raka’a ta farko, haka zai yi ta biyu; ba ragi ba qari. 
 1. Bayan kuma ya qare sujada ta biyu a cikin raka’a ta biyu,

sai ya zauna don yin tahiya ta farko. Ga lafuzzanta kamar haka: “Attahiyátu lilláhi; was-salawátu wax-xayyibátu. Assalámu alaika ayyuhan-Nabiyyu wa rahamatul-Láhi wa barakátuhu. Assalámu alainá, wa alá ibádullahis-sálihína. Ash-hadu al-lá iláha illal-Láhu, wa ash-hadu anna Muhammadan abduhu wa rasúluhu.” 

 1. Sa’annan ya tashi domin ya cika abin da ya yi saura na sallarsa idan sallar da yake kanta mai raka’a uku ce ko huxu.  

 Illa dai kawai a raka’a ta uku da ta huxu, ba zai wuce karanta Fatiha ba kawai.

 • Amma idan salla mai raka’a biyu ce yake yi kamar sallar Subahin, to, tahiyar qarshe xin nan, kamar yadda aka bayyanata a sama, ita ce kawai a kansa.

 1. Sa’anna a cikin raka’a ta qarshe bayan kammala sujada ta biyu, 

sai ya zauna don yin Tahiya ta qarshe. Zai kuma yi ta ne kamar yadda ya yi ta farko. Xan qarin da yake akwai kawai shi ne na salati ga Annabi sallallahu alaihi wa salla, kamar haka: “….Allahumma salli alá Muhammadin wa alá áli Muhammadin kamá sallaita alá Ibrámina wa alá áli Ibráhíma innak Hamídun Majid. Wa bárik alá Muhammadin wa alá áli Muhammadin kamá bárakta alá Ibráhima wa alá áli Ibrámíma innaka Hamídun Majídun.” 

 • An kuma so, bayan haka, ya qara da faxar: “A’uzu billáhi min azábil Jahannama, wa min azábil qabri, wa min fitinatil mahyá wal mamáti, wa min fitnatil-masíhi addaj’jal.” Bayan haka kuma sai ya roqi duk abin da yake so. 
 1. Sa’anna ya juya ya fuskanci dama gare shi, ya kuma ce:

 “assalámu Alaikum wa rahamatullahi.”  Sa’annan ya koma wajjen hagu ya sake faxin haka.

Ita kuwa sallama, da zarar Musulmi ya kai gare ta, to, ya kamala sallarsa kenan. Wannan shi ne abin da ya tabbata daga bakin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, cewa: “Salla na farawa ne da kabbara, tana kuma qarewa da sallama.”[Abu dawuda:61/ Tirmizi:3]. A wata Hausa, wannan magana ta manzon Allah Sallahu alaihiwa sallam na nufin, da zarar muslmi ya ce: ‘Allahu Akbar,’ to, komai ya haramta gare shi, wanda salla ba. Idan kuma ya kai gavar da ya ce: ‘Assalamu Alaikum,’ to, komai kuma ya halasta gare shi, na halas.    

 1. An kuma so, a duk bayan sallar farilla, Musulmi ya karanta abubuwa kamar haka:
 1. Istigfári “astagfurullah” qafa uku.
 2. Sa’annan ya ce: “allahumma antassalam wa minkassalam tabárakta yá zal-jaláli wal ikrám”, “allahumma lá máni’a lima a’axaita, walá mu’uxí lima mana’ata, walá yanfa’u zaljiddi minkal jaddu” 
 3. Sa’annan ya faxi: “subhanalláhi” sau talatin da uku “33), da “alhadu lilláhi” sau talatin da uku “33”, da “alláhu akbar” sau talatin da uku “33”. Qarshe kuma ya kamala da faxar: “lá’iláha illal-láhu wahdahu, lá sharíka lahú, lahul-mulku wa lahul hamdu wa huwa alá kulli shai’in qadírun”  

Me Wanda Bai Hardace Fatiha da Waxannan Zikirora ba Zai yi? 

 • Ya zama wajibi a kan irin wannan Musulmi, ya yi qoqari iyakar zarafi ya gay a hardace irin waxannan zikirora, da karanta su yake wajaba a cikin salloli da bayansu. Ya kuma sani, wajibi ne ya hardace su da harshen Larabci; ba za a karvi wani harshe wanda ba shi ba. Ga zikiroran kamar haka:
 • Fatiha, da kabbara, da subhana rabbiyal-azim, da sami’allahu liman hamidah, Rabbana wa lakal-hamdu, da subhana Rabbiyal’a’alah, Rabbig-fir lí. Tahiya da salati ga Annabi, Assalamu Alaikum wa rahamatullahi wa barakátuhú.   
 • Amma, wajibi ne a kan muslmi, kafin Allah yah ore masa hardace waxannan zikirora, ya riqa maimaita tasbíhi “subhanallah”, da tahmídi “alhamdu lillah”, da takbíri “allahu akbar”, waxanda ya iya, a lokacin da yake salla, ko ya riqa maimaiya duk ayar da ya hardace a lokacin da yake tsaye. Yin haka biyayya ne ga Umarnin Allah Maxaukakin Sarki da ya ce: “To, sai ku ji tsoron Allah gwargwadon ikonku”[Tagabun:16].
 • A xan wannan tsakani, yana da kyau matuqa gare shi, ya mayar da hankali ga yin salla a cikin jama’a, domin ya samar wa sallalrsa nagartancen guubi, saboda irin yadda liman yake xauke nauyin wani yanki na kasawar dad a take tare da mamu. 

دليل المسلم الميسر

موقع دليل المسلم الميسر هو نسخة الكترونية من كتاب (دليل المسلم الميسر) وهو أحد مشاريع شركة الدليل المعاصر وتم إنتاجه بأكثر من ١٥ لغة وتم توفير المحتوى في عدد من القوالب الالكترونية المميزة.

Modern Guide