You are here

Dalilin Samar da Halittarmu

×

Error message

Deprecated function: Function create_function() is deprecated in views_php_handler_field->pre_render() (line 202 of /var/www/drupal7-websites/sites/all/modules/contrib/views_php/plugins/views/views_php_handler_field.inc).
man pray in the mosque

Da yawa daga cikin masana zaqaqurai a fagen tunani, su da fararen hula, kafaxa da kafaxa, sukan saui kansu a cikin ruxani da rashin sanin makama, idan suka yi qoqarin amsa waxansu muhimman tambayoyi da suke da alaqa ta qud-daqud da rayuwarmu, waxanda suka haxa da cewa:  

Mene ne dalilin da ya sa aka halicce mu?

Wace manufa muke da ita a rayuwarmu?

Alqur’ani mai girma ya daxe da yin cikakken bayanin manufa da dalilin da ya sa Allah Maxaukakin Sarki ya halicci xan Adam ya kuma sawwaqe masa wannan rayuwa. Wannan bayani yana qunshe ne a cikin faxar Allah Maxaukakin Sarki: “Ban kuma halicci aljanu da mutane ba, sai kawai don su bauta mani” [Zariyat:56]  Wannan aya ta nuna mana cewa, bautar Allah ita ce kaxai dalilin da ya sa Allah Maxaukakin Sarki ya halicce mu a bisa doron qasa. Duk wani abu kuma, wanda ba ‘ibáda’ ba to, xan rakiya ne gare ta; wajibi ne ya zama yana share mata hanyar tabbata da kama qasa ne.  

Sai dai ibada a mahangar Musulunci, ba tana nufin ruhbániyya ba. Ita ce, a wayi gari mutun ya yanke alaqa da duk wani fanni na jin daxi da more ma rayuwar duniya. Ko alama ba haka al’amarin yake ba. Ibada a Musulunci, ta haxa Sallah, da Azumi, da Zakka, da duk wani motsi da xan Adam zai yi a bisa doron qasa, ayyuka da duk wani fannin ci gaba da zai samar, da kuma sauran hulxoxi da alaqoqinsa na yau da kullum. Kai! har ma da wasanni da sauran nau’ukan jin daxi irin na rayuwa. Duk waxannan abubuwa, a mahangar Musulunci, sunansu ibada matuqar an aikata su da kyakkyawar niyya da kuma ingantattar manufa. Wannan shi ne dalilin da ya sa Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya furta cewa: “Idan xayanku ya yi aure sadaqa ne.” [Buhari:1006]  Wato, yana nufin Musulmi yana samun lada har akan saduwarsa da iyalinsa.    

Da wannan manufa kuwa, za a fahimci cewa, ibada, bayan zaman ta babbar manufa a rayuwar duniya, to, babu ma wani abu a cikin gaba xayan rayuwar, farkonta har qarshe, wanda ba ibada ba. Saboda haka, Musulmi, matuqar ya karva sunansa, duk inda ya samu kansa a fagen rayuwa, to, yana bautar Ubangijinsa ne. Tabbacin wannan kuwa, shi ne faxar Allah Maxaukakin Sarki: “Ka ce: Lalle ne sallata, da yankana, da rayuwata, da mutuwata, na Allah ne Ubangijin talikai” [An’am:162]  

دليل المسلم الميسر

موقع دليل المسلم الميسر هو نسخة الكترونية من كتاب (دليل المسلم الميسر) وهو أحد مشاريع شركة الدليل المعاصر وتم إنتاجه بأكثر من ١٥ لغة وتم توفير المحتوى في عدد من القوالب الالكترونية المميزة.

Modern Guide