You are here

Babu Shamaki Tsakanin Bawa da Ubangijinsa

×

Error message

Deprecated function: Function create_function() is deprecated in views_php_handler_field->pre_render() (line 202 of /var/www/drupal7-websites/sites/all/modules/contrib/views_php/plugins/views/views_php_handler_field.inc).

Da yawa daga cikin addinai sun ba wa wani sashe na wasu xaixaikun mutane wata daraja, ta hanyar fifita su a kan saura da sunan addini. Suka ta’allaqa ibadoji da imanin mutane a kan yarda da amincewar waxannan shafaffun da mai. Su waxannan mutane, a tsare-tsaren waxannan addinai, suna a matsayin wani shamaki ne tsakanin sauran bayin Allah da Ubangijinsu. Su suke bayar da lasisin samun gafara. Tana yiwuwa ma wasu daga cikinsu, su raya cewa, sun san gaibi, kamar dai yadda suka saba kururutawa da yayatawa irin wannan mummuna kuma gurvatacciyar aqida. Duk kuma wanda ya sava musu, sun yanke masa hukuncin haxuwa da hasara da tavewa, bayyanannu. 

Ana cikin haka, sai Musulunci ya bayyana, ya xaukaka darajar xan Adam ya kuma mutunta shi, ta hanyar rusa irin wancan tsari, da ya sanya arzikin mutane, da samun karvar tuba, da sauran ibadojinsu a hannun waxansu xaixaikun mutane. Duk kuwa irin matsayi, da xaukaka da nagartar da suke da ita, wannan bai dami Musulunci ba.   

A haka sai aka wayi gari, bautar duk da Musulmi zai yi tsakanin sa da Ubangijinsa, babu wani mahaluki daga cikin mutane da yake da hannu a matsayin wani shamaki ko tsakani a ciki, balle ya yi masa alfahari. Allah subhanahu wa ta’ala kusa yake sosai da bayinsa. Duk wanda ya kira shi daga cikin su, yana jin sa, zai kuma karva masa. Sane kuma yake, Maxaukakin Sarki, da irin bauta da sallar da yake yi domin sa, zai kuma ba shi lada a kan haka. Babu kuma wani mahaluki daga cikin mutane, da yake da haqqi da ikon ba wa wani takardar shaidar gafara da karvar tuba. Duk lokacin da bawa ya tuba, ya kuma tsare sharuxxanta da alfarmarta, to, shakka babu, Allah zai gafarta masa. Babu wanda yake da wani qarfi gagara-misali, ko ikon yin wani tasiri a cikin wannan sarari na subhana: komai yana hannun Allah.  

Haka ne Musulunci ya ‘yanta hankalin Musulmi ta hanyar ba shi cikakkiyar dama ta yin tunani da batun zuci, da komawa ga Alqur’ani da ingantattun Hadisan Annabi sallallahu alaihi wa sallam don neman kowane irin hukunci, a duk lokacin da suka sami wata banbancin fahimta. Babu mahaluki daga cikin mutane da yake da lasisin cewa, ya zama wajibi a saurara a kuma yi biyayya ga duk abin da ya yi umarni da shi, sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, saboda shi ba ya faxin son ransa; sai abin da Allah Maxaukakin Sarki ya yi masa wahayi ya kuma xora shi a kan tafarkinsa. Tabbacin wannan kuwa shi ne faxar Allah Maxaukakin Sarki: “Kuma bay a yin magana daga son zuciya. Maganarsa bat a zamo ba, face wahayi ne da ake aikowa” [Najm:3-4]  

Kai! Mun dai gode wa Allah Maxaukakin Sarki a kan wannan ni’ima da ya yi mana ta addinin Musulunci, waddad babu kamarta, a matsayinsa na addinin da yake tafiya kafaxa-da-kafaxa da bukatu irin na tsarin xan Adam, na azaliyya, ta hanyar xaukaka martabarsa da damqa masa ragwamar gudanar da rayuwarsa da kansa bayan ya ‘yanto daga qangin baqar bauta da qanqan da kai ga wani, wanda ba Allah Maxaukakin Sarki ba.

دليل المسلم الميسر

موقع دليل المسلم الميسر هو نسخة الكترونية من كتاب (دليل المسلم الميسر) وهو أحد مشاريع شركة الدليل المعاصر وتم إنتاجه بأكثر من ١٥ لغة وتم توفير المحتوى في عدد من القوالب الالكترونية المميزة.

Modern Guide