You are here

Ana Lura ne ta Tantagaryar Manufofin Musulunci ba Ynayin Rayuwar Wasu Musulmi ba.

×

Error message

Deprecated function: Function create_function() is deprecated in views_php_handler_field->pre_render() (line 202 of /var/www/drupal7-websites/sites/all/modules/contrib/views_php/plugins/views/views_php_handler_field.inc).

Yau idan ka yi kicivis da wani likita, yana aikata wani abu da yake cutar da lafiyar xan Adam. Ko wani malami yana waxansu halaye da ba su dace ba. A matsayinka na wanda ya san matsayi da muhimmancin waxannan fannona guda biyu, tattare da irin yadda za ka sami damuwa da qyamar waxannan xabi’u nasu sakamakon masaniyar da kake da ita da waxacan fannoni. Hakan ba za ta sa ka canza matsayin yadda ka fahimci muhimmancin da likitanci da karatu da karantarwa suke da su ga rayuwar xan Adam; bunqasawa ta shimfixa nagartaccen tsari ba. 

Iyakar abin da za ka fahimta shi ne, wancan likita da malami, ba kowa ba ne illa hoton mutanen da ba su san martaba da darajan fannonan ilimin da suke wakilta ba.

To, kamar haka ne al’amarin yake ga abin da ya shafi addinin Musulunci. Yau idan ni ko kai, xayanmu ya ci karo da wasu xaixaikun Musulmi suna gudanar da wasu miyagun xabi’u. Muna da yaqini da tabbacin cewa, wannan ba shi ne cikakken hoton nagartaccen tsarin Musulunci ba. Iyakar abin da za mu fahimta shi ne, waxannan halaye da suke aikatawa, una bayyana irin yadda su, a qashin kansu suke da rauni a matsayinsu na ‘ya’yan Adamu, waxanda suke tattare da waxansu halaye da xabi’u, da ba su da wata alaqa da Musulunci, kamar yadda halayen wancan likita da malami, ba su wata alaqa da fannin likitanci da na karantarwa.  

دليل المسلم الميسر

موقع دليل المسلم الميسر هو نسخة الكترونية من كتاب (دليل المسلم الميسر) وهو أحد مشاريع شركة الدليل المعاصر وتم إنتاجه بأكثر من ١٥ لغة وتم توفير المحتوى في عدد من القوالب الالكترونية المميزة.

Modern Guide