You are here

Matuzgan Shari’ah A Musulunci

×

Error message

Deprecated function: Function create_function() is deprecated in views_php_handler_field->pre_render() (line 202 of /var/www/drupal7-websites/sites/all/modules/contrib/views_php/plugins/views/views_php_handler_field.inc).

Musulmi duk inda suke a faxin duniya, suna dogara ne a kan waxansu manya-manyan tuwasu da dalilai, domin sani da tsago hukunce-hukuncen Shari’ar Musulunci. Ta waxannan hanyoyi ne kuma suke sama wa sauran abubuwan da suke faruwa a rayuwarsu ta yau da kullum, waxanda Shari’a bat a bayyana hukuncinsu, filla-filla ba, matsayin zama halas ko haram.  

Manya-manyan Matuzgan Hukunce-hukuncen Shari’ah su ne kamar haka:

 1. Alqur’ani Mai Girma: 

Alqur’ani mai girma shi ne littafin Allah Maxaukakin Sarki, wanda ya saukar wa bayinsa, domin ya zama shiriya a gare su, a matsayinsa na mai rarrabewa tsakanin qarya da gaskiya, ta hanyar yin cikakkiyaen bayani a kan kowanne daga cikinsu. Littafi ne kuma da Buwayayyen sarkin ya ba wa cikakkiyar kariya, ta yadda babu wani abu da yake iya gurvatawa ko canza shi. Ya kuma zama wajibi a kan gaba xayan Musulmi, yin biyayya ga duk umarce-umarce da hane-hanen da duk, Allah Maxaukakin Sarki ya yi a cikin wannan littafi. Idan muka taras a cikinsa ya ce: “Kuma ku tsayar da Sallah”[Annur:56], to, hakan tana tabbatar muna cewa, lalle Sallah wajibi ce a kanmu. Idan kuma ya ce: “Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfasha ce, ta kuma munana ga zama hanya”[Isra’i:32], hakan ta tabbatar mana da cewa, zina haramun ce. Tunda kuwa har Allah Maxaukakin Sarki ya xauke nauyin kula tare da kiyaye Alqur’ani daga duk wani canji; qari ko ragi, to, babu abin da muke da buqata das hi, illa tabbatar da zaman aya, hujja da dalili a kan duk abin da ake a kansa.  

 1. Sunnar Annabi:  

Sunnah kuma na nufin duk zancen da ta tabbata cewa, Annabi sallallahu alaihi wa sallam ne ya furta shi, ko ya aikata, ko aka aikata ko aka furta, yana ji yana kuma ganai, amma bai musa ba, da kuma sauran halaye da xabi’unsa. To, da zarar mun tabbatar da inganci da tabbatar fitowar zance daga bakinsa mai tsarki, sallallahu alaihi wa sallam,  kamar faxarsa: “Ba a haxa mace da xaya daga cikin innoninta ko gwaggwoninta.” [Buhari:5109]. To, daga nan mun tabbatar da cewa, ba ya halasta ga mutum, yana aure da wata mata, ya kuma auro wata Inna ko gwaggwonta.     

Idan kuma za a leqa Sunnar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam  don tsago wani hukunci, to, ba za a yi haka ba, sai an tabbatar da samuwar abubuwa guda biyu da suka haxa da:

 • Tabbatar da cewa, lalle da aka ce wannan zancen Manzon Allah ne, sallallahu alaihi wa sallam, hakan gaskiya ne. Domin tabbatar da irin wannan manufa ne, malaman Musulunci magabata, suka bayar da matuqar qoqari, ta hanyar shimfixawa da samar da nagartattun hanyoyi don yin nazarin qwaqwaf, da tantance ingancin zantukansa masu alfarma. A iya banbancewa tsakanin Hadisai ingantacci, waxanda riwayarsu ta taho tab akin amintaccin malaman riwaya, waxanda suka sami cikakkiyar shedar rashin mummunar mantuwa da rafkanuwa. Aka banbance tsakanin irin waxannan Hadisai, da irin kwashe-kwashen da aka jingina wa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, alhali bai ji bai kuma gani ba; ba sunnarsa ne ba. Illah dai kawai sun samu ne sakamakon kurakurai, da rafkanuwa, ko a bisa qiren qarya daga wani rukuni na maqiya Musulunci.        
 • Tabbatar da zaman Hadisin  hujja da dalili a kan zancen da ake a kai. irin wannan hujja kuwa ta kan zo qarara, ba tare da ma’anarta ta haxu da wata hawa da gangara ba ko savani ba. tana kuma yiwuwa sanadarin da Hadisin yake qunshe das hi, ya iya xaukar ma’ana fiye da xaya. Tana kuma iya fanxarewa, ta yadda ba za iya fahimtar tab a, sai an haxa hancinta da na ‘yar’uwarta da take qunshe a cikin wani Hadisin na daban. 
  .
 1. Ijmá’i:

Shi kuwa ijmá’i yana nufin qarshen abin da kan gaba xayan amintattun malaman Musulunci, ya haxu a kai, a daidai wani kevantaccen zamani daga cikin zamunnan Musulunci. Mafi yawan kuma hukunce-hukuncen Musulunci da Shari’o’onsa, sun sami wannan tagomashi na haxuwar kan malaman Musulunci; ba a sami savani ba a cikinsu. Daga cikin irin waxannan hukunce-hukunce akwa kamar, adadin raka’o’in salla, da lokacin da ya kamata a tsayar da sahur, da kuma wanda ya kamata a sha ruwa a cikinsa, a lokacin Azumin watan Ramalana. Haka kuma da nisabin Zakka a cikin zinari da azurfa, da waxansu hukunce-hukunce waxanda ba waxannan ba.    

Haka kuma idan kan sahabbai ko na tabi’ai, ya haxu a kan wani hukunci, to, hakan babban dalili ne da yake tabbatar da ingancinsa, saboda bat a yiwuwa gaba xayan al’umma ta haxu a kan kuskure.

 1. Qiyási:

Qiyási kuma yana nufin yanke wa wata matsala, wadda babu hukuncinta qarara a cikin Alqur’ani da Sunna,  hukunci. Ana kuma yin haka ne ta hanyar xauko wani yankakken hukunci na wata matsalar, wadda suka yi tarayya da ita wannan xin, a cikin tuwasu da rassa da dalilai, sai a auna, a yanke mata. Misalin wannan kuwa shi ne, kamar a ce, haramun ne a daki mahaifa, tunda anka haramta tankiya da xaga murya a kan tasu, kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki ya ce: “Kada ka ce musu tir, kada kuma ka yi musu tsawa”[Isra’i:23]. Ma’anar wannan kuwa shi ne, tunda dai har Allah Maxaukakin Sarki ya haramta xaga murya a kan ta mahaifa don kada a cutar das u, to, kuwa haramcin dukansu shi ne mafi qamari da cancanta, saboda kowane xaya daga ayyukan yana matuqar cutar da su. Wannan karatu kuwa babi ne mai matuqar faxi da zurfi, ta yadda sai manya-manyan malamai, sha-fannoni qwararru a fagen, ke iya ratsawa da keta hazonsa. Ta haskensa ne kuma ake iya ganowa da tsago hukunce-hukuncen sabbib matsalolin zamani.  

Me ya sa Malamai Suke Savani Tattare da Haxuwar Kansu a Kan Matuzgan Shari’ah?

Domin sanin amsar wannan tambaya, wajibi ne ka san abubuwa kamar haka:

 1.  Babu savani tsakanin gaba xayan ma’abuta  ilimi a kan abin da ya shafi ‘imani’ ginshiqai, rukunai da abubuwan da suke walwale shi. Haka kuma tuwasu da matuzgan Shari’o’i, da rukunan Musulunci da sauran manyan rassansa, duk, babu savani tsakaninsu a kansu. Inda kawai wannan savani yake shi ne a cikin wani sashe na rassan hukunce-hukuncen fiqihu da yadda ya kamata a aiwatar da su.    

Amma, manya-manyan qa’idoji da tuwasun hukunce-hukunce, da suka shafi Shari’ar Musulunci a matsayinta na cikamakin Shari’o’i da saqwanni, wadda kuma Buwayayyen Sarkin ya xauki nauyin kare mutunci da alfarmarta har zuwa ranar da za a busa qaho. A cikin ikon Allah Maxaukakin Sarki da iyawarsa, babu inda kan ma’abuta ilimi ya rabu a cikinsu.

 1.  Shi kuwa savani a cikin rassan   hukunce-hukunce sakamakon sharhi da bayaninsu, abu ne gadadde a xabi’ar xan Adam. Saboda haka ne ma, babu wata Shari’ah saukakka daga wurin Allah, ko wadda xan Adam ya shata wa kansa, da ta tsira daga wannan. Kai! babu ma wani fanni na ilimi a bisa doron qasa, da babu irin wannan savani a cikinsa. Malaman tsare-tsaren dokoki, gaba xayansu, za ka taras suna qara wa junansu sani, ta hanyar banbance-banbancen ra’ayota da fahimta a lokutan da suke sharhi da fashin baqi. Haka su ma Kotuna, ba bisa godabe xaya suke aiwatar da dokokinba. Malaman Tarihi ma, ba a bar su a baya ba, har kullum suka sami savani a cikin riwayoyi da irin yadda al’amurra suka faru. Ba zancen ma waxannan, har likitoci, da injiniyoyi, da masana Adabi, bakunansu da sukan tafi bai xaya ba a cikin dukan babuka. Za ka taras, a fagen nazari da yanyana da tsettsefe maulu’i xaya, kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa.      

Saboda haka, savani a cikin qananan al’amurra, rassa, abu ne gadadde, wanda yakan faru sakamakon tsarin rayuwar ilimi da aiki, na azaliyya. 

 1.  Sai dai yana da kyau a sani, Allah Maxaukakin Sarki ya yi rangwame da duk wanda ya hau ingantaccen godabe don nemi gane gaskiya, amma, ya sami kuskure; ba zai kama shi da wani laifi ba. Ta tabbata cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, ya yi wa duniyar masu binciken gaskiya da gaskiya bushara, cewa, xayansu duk ba zai tashi tutar babu ba; haqarsa ta cimma ruwa ko ba ta cimma shi ba.   

Idan Allah ya saakamaon bincikensa, ya dace da gaskiya, to, yana da lada biyu. Idan kuma Allah bai nufe shih aka ba, ya kuskure gaskiya tattare da kwaxayin da yake cike da ransa na samun haka, da irin yadda ya qanqame tafarkin gaskiya, to, yana da lada xaya. A kan haka ne Annabi sallallahu alaihi wa sallam, ya ce: “Idan shugaba ya yi ijitihadi domin yanke wani hukunci, ya kuma dace da gaskiya, to, yana da lada biyu. Idan kuma ya kuskure, to, yana da lada xaya.”[Buhari:7352]. 

Misalin wannan shi ne labarin da Allah Maxaukakin Sarki ya bayar naAnnabawansa guda biyu, Annabi Dawuda da Sulaimanu alaihimassalam, a lokacin da aka kawo musu wata matsala. A qoqarin samar mata da hukunci, sai kowanensu ya yi ijtihadi a qashin kansa. A qarshe kuma sai hukuncin da Sulaimanu alaihissalam, ya yanke, ya zama shi ne daidai, a lokacin da shi kuma Dawuda alaihissalam, bai sami muwafaqa ba. Da Allah Maxaukakin Sarki ya tashi bayar da labarinsu, sai ya tabbatar da ingancin hukuncin Sulaimanu da zaman na Dawuda ba daidai ba, alaihimassalam. Sai dai kuma tattare da haka, Allah Maxaukakin Sarki, sai ya yi jinjina da yaba wa wannan qoqari nasu, tare da tabbatar da zamansu masu ilimi. Wannan ma’ana kuwa tana qunshe ne a cikin faxarsa Maxaukakun Sarki: “Sai muka fahimtar da Sulaimana ita. Dukansu kuma, mun ba su hukunci da ilimi”[Anbiya:79]   

 1.  Gaba xayan zantukan malamai ma’abuta ilimi kuma, ba abin sakawa kwandon shara ba ne, saboda dukan malaman da suka kafa Mazhabobi guda huxu xin nan da ka sani, suna dogara ne a kan Alqur’ani da Hadisi a cikin tsago hukunci; ba za su bayar da fatawa ba, ko kushe wata, sais aka waxannan tuwasu gaba. Savanin da yake faruwa a tsakaninsu na fahimta, ba abu ne da suke ginawa a kan makahon ra’ayi, da son zuciya don cimma wata buqata ta duniya ba, ko alama! Tsabar ilimi da tsoron Allah, da qoqarin kaiwa ga tantagaryar gaskiya, su ne tuwasun irin wannan savani. Za taras cewa, wani Hadisi ya sadu da wani daga cikinsu, a yayin wani kuwa ko labarinsa bai tava samu ba. Ko kuma a sami banbaci tsakaninsu sakamakon irin baiwar da Allah ya yi wa kowannensu ta ilimi da basira da fahimta. To, sai ka taras kowanensu, a qoqarin nazarin wani dalili ko wata hujja a cikin wani Hadisi ko wata aya ta Alqur’ani, ya fahimci wani abu savanin na xan’uwansa. Da dai sauran abubuwa masu kama da waxannan.  
 2. To, daga cikin manya-manyan malamain fiqihun Musulunci, huxu ne suka yi fice, waxanda kuma mutane suka yarda da zamansu limamai a fagen ilimi da addini. Gaba xayan waxannan malamai kuma, ka sani, sun kai matuqa a fagen ilimi, da sanin makamar addini, da kuma tsananin bautar Allah da tsoronsa. Almajiransu kuma ba su da iyaka, sun kuma yaxa ilimi da zantukan da suka xauka daga gare su, a cikin faxin duniya. Sakamakon haka ne kuma, aka wayi gari, manya-manyan Mazhabobin Musulunci guda huxu, na wasu malamai daga cikinsu, sun sharaha sun kuma bazu a qasashen Musulmi. Waxannan  malamai kuwa su ne:
 •  Imamu Abu Hanifata:  Cikakken sunansa shi ne, Nu’umanu xan Sabitu. Ya rayu a qasar Iraqi ne, ya kuma kwanta dama a shekara ta 150 bayan hijira. Idan kuma ka ji an ce, Mazhabar Hanafiyya, to, shi ake nufi. 
 • Imamu Maliku xan Anad Al-asbahí:  Ana yi masa laqabi da ‘Babban Malamin Madina.’ Ya rasu a shekara ta 179 bayan hijira. Shi ne wanda ya assasa Mazhabar Malikiyya.
 •  Imamu Shafi’i: Cikakken sunansa shi ne, Muhammadu xan Idirisu. Ya rayu tsakanin Makka da Madina da Iraqi da kuma Masar. Allah ya karvi rayuwarsa a shekara ta 204 bayan hijira.
 • Imamu Ahmad xan Hambali: , Imamu Ahmad xan Hambali: Mafi yawan rayuwarsa ya yi ta ne a Iraqi, ya kuma rasu a shekara ta 241bayan hijira. Shi ne kuma wanda ya kafa Mazhabar Hanbaliyya.

Abin ban sha’awa ma duk, bai irin yadda ake da fahimta da girmama juna tsakanin waxannan malamai a hannu xaya ba, da kuma tsakanin almajiransu a xayan hannu. Kowane daga cikinsu yana yabawa tare da jinjina wa x an’uwansa, da kuma karva da yarda da nazarin fahimtar juna. Kowannensu yana kwaxayi ne da qoqarin gano gaskiya da yin biyayya gareta. Saboda haka ba shi da wata damuwa idan fahimtarsa ta dace da ta wane a cikin wata mas’alah,wata kuma ta dace da ta wane, bisa tafarkin gaskiya da qarfin hujja. Tabbacin haka shi ne, irin yadda tarihi ya tabbatar da yadda, wasu daga cikinsu, suka zauna gaban wasu, suka xauki karati a matsayin almajirai, kamar Imamu Ahmad. Tarihi ya gaya mana cewa ya yi xalibta a gaban Imamu Shafi’i. Shi kuma Sahafi’i ya yi a hannun Imamu Maliku. Shi kuma Imamu Maliku, akwai sanayya da musayar ilimi tsakaninsa da almajiran Imamu Abu Hanifata. 

Ta kuma tabbata cewa, babu xaya daga cikin waxannan jigajigan malamai, wanda bai bayyana wa duniya ba, cewa: Da zarar Hadisi ya inganta, to, na yarda na kuma  amince da hukunci da yake xauke da shi; Mazhabata ne. Ashe kenan baban gurinsu na farko, shi ne yaxa ilimi da kawar da jahilci daga tsakanin mutane. Ikon Allah! Muna roqon Allah ya yi masu rahama irin wadda ba ta da iyaka.   

To, Mene ne yake Wajaba a Kan Musulmi Dangane da Savanin Malamai a Duniyar Fiqihu?

Babu abin da yake wajaba a kan Musulmi, illa qudurcewa a ransa cewa, yana neman gane gaskiya ne da biyarta..

 • Idan almajiri ne shi, irin wanda qafarsa ta kama qasa, qwararre kuma a fannin gane yadda ake tsago hukunci, to, sai ya tsaya a kan duk abin da qoqari da nazari da bincikensa ya kai shi ga ganowa, gwargwadon qa’idojin da malaman usulul-fiqhi, suka shimfixa. Haramun kuma a kan, ya xauki wani qabilanci ga wani mutum ko Mazhabarsa, idan ya gama gane cewa, gaskiya tana tare da wane, alhali ba tare suke ba.     
 • Shi kuwa wanda yake sahun ya’ayyuhan-nasu, daga cikin Musulmi; bai qware a wannan fage ba, balle qafarsa ta kama qasa, ta yadda zai iya cin gashin kansa a fagen nazati da tsago hukunci, to, ya zama wajibi a kansa ya yi iya qoqarinsa na aiki da xayan Mazhabobin nan, wadda duk hankalinsa ya kwanta da ita dangane da lafiyar addininsa da iliminsa. Idan ya yi haka, to, ya xauke nauyin da yake kansa, tunda ya yi biyayya ga umarnin Allah Maxaukakin Sarki da ya ce: “Sai ku tambayi ma’abuta ilimi idan kun kasance ba ku sani ba”[Anbiya:7]

To, da zarar hankalinsa ya kwanta a kan wani zance da ya ci karo da shi, ko kuma ya tambayi wani amintaccen malami a kan wata matsala, to, ba dole sai ya sake tuntuvar wani malamin ba. Idan kuma dama can yana da masaniya da wani hukuncin, savanin wanda ya samu yanzu, to, abin da yake wajaba a kansa, shi ne, xauka da amfani da wanda ya fi hangen zamansa mafi kusa ga gaskiya. Wato, kamar dai irin matakin da maras lafiya, ke xauka idan likitoci daban-daban suka xora shi a kan magunguna daban-daban.  

Wajibi ne kuma ya nisanci aibantawa ko ganin la’arin wani Musulmi xan’uwansa, da yake kan wata fatawa savanin wadda shi yake a kai, matuqar dai shi ma wancan yana kan wata Mazhaba ta fiqihu, ko yana koyi ne da wani malami amintacce, ko kuma xaya ne shi daga cikin waxanda qafarsu ta kama qasa a fagen fiqihu da ijtihadi. Sahabbai da sauran magabata ma suka sami irin wannan banbancin fahimta a fagen fiqihu, amma hakan ba za ta tava danqon zumunci da soyayyar  da suke tsakaninsu ba. Suka kuma tafka muhawara har hanci ya yi zafi, ba tare da wani ya ga la’arin wani ba.   

دليل المسلم الميسر

موقع دليل المسلم الميسر هو نسخة الكترونية من كتاب (دليل المسلم الميسر) وهو أحد مشاريع شركة الدليل المعاصر وتم إنتاجه بأكثر من ١٥ لغة وتم توفير المحتوى في عدد من القوالب الالكترونية المميزة.

Modern Guide